Lagarde ta zama sabuwar shugabar asusun bayar da lamuni na duniya

Christine Lagarde Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Christine Lagarde, sabuwar shugabar IMF

Asusun bada lamunin IMF, ya nada Christine Lagarde a matsayin sabuwar shugabarsa. Kakakin IMF din kenan yana bada sanarwar zaben Christine Lagarde a matsayin sabuwar shugabar asusun har tsawon shekaru biyar masu zuwa.

Bakin hukumar zartaswar IMF din ya zo daya, wajen zaben Christine Lagarde, wadda a halin yanzu ita ce ministar kudin Faransa.

Madame Lagarde ita ce mace ta farko da ta taba rike daya daga cikin manyan hukumomin kudade na duniya.

Tun farko a yau nadin nata ya kusan zama dimun, bayan da Amirka - wadda ita ce ta fi ba asusun gudunmawa - ta fito fili ta goyi bayanta.

Mutumen da Christine Lagarde zata gada, Domininique Strauss Kahn, yayi murabus ne bayan an zarge shi da kokarin yiwa wata mata fyade.