Jonathan ya mika sunayen ministoci ga Majalisa

Jonathan
Image caption A watan Mayu ne aka rantsar da Goodluck Jonathan

Shugaban Najeriya Goodluck Jonathan ya mika sunayen mutane 34 da yake son nadawa ministoci ga Majalisar Dattawa ciki harda tsohuwar ministar mai Deziani Alison-Madueke da na kudi Olusegun Aganga.

Shugaban Majalisar Sanata David Mark ya karanta sunayen a gaban Majalisar, amma ba tare da ma'aikatun da za su jagoranta ba.

Ana sa ran Jonathan zai mika ragowar sunayen domin kammala sunayen majalisar ministocin.

Wata guda kenan da rantsar da shugaba Jonathan, kuma ana sa ido sosai kan sunayen ministocinsa a ciki da wajen kasar - musamman ga masu zuba jari.

Har da shugaban PDP

13 daga cikin sunayen tsaffin ministoci ne a gwamnatin da ta gabata, yayin da sabbi daga cikinsu suka hada da Barth Nnaji, wanda a baya shi ne mai baiwa shugaban shawara kan harkokin wutar lantarki.

Akwai kuma shugaban jam'iyyar PDP mai mulkin kasar Dr Bello Halliru Mohammed.

Jonathan ya nemi Majalisar da ta gaggauta amincewa da sunayensu.

Kuma daga nan ne zai raba musu ma'aikatun da za su jagoranta.

A baya wata majiya ta nuna cewa Jonathan ya tattauna da tsohuwar ministar kudin kasar Ngozi Okonjo-Iweala, domin ta kasance a sabuwar majalisar.

Sai dai sunanta baya cikin wadanda aka gabatar.

Cikakken jerin sunayen da aka mika:

Zainab Ibrahim Kuchi (Niger), Viola Onwuliri (Imo), Mrs. Stella Odua-Ogiemwonyi (Anambra), Mrs. Erelu Olushola Obada(Osun), Olusegun Aganga (Lagos), Mike Onolememen (Edo), Abba Moro (Benue), Olugbenga Ashiru (Ogun) Akinwunmi Ayo Adesina (Ogun), Dr Samuel Ortom (Benue), Diezani Allison-Madueke (Bayelsa) Ruqayyatu Rufai (Jigawa), Godsday Orubebe (Delta) Bala Mohammed (Bauchi), Shamsuddeen Usman (Kano), Bello Halliru Mohammed (Kebbi), Bukar Tijjani Zannah (Borno), Mrs Jumoke Akinjinde (oyo).

Akwai kuma Yarima Lawal Ngama (Yobe), Emeka Nwogu (Abia), Mohammed Bello Adoke (Kogi), Barth Nnaji (Enugu), Labaran Maku (Nasarawa), Tonye Cole (Rivers), Onyebuchi Chukwu (Ebonyi), Bolaji Abdullahi (Kwara), Caleb Olubaolade (Ekiti), Bashir Yuguda (Zamfara), Yusuf Sulaiman (Sokoto), Mohammed Musa Sada (Katsina), Obadiah Ando (Taraba), Abdullahi Idris Umar (Gombe), Zainab Maina (Adamawa), Ita Okon Bassey Ewa(Akwa Ibom).