Nato ta kai hari a wani otal a Kabul

Hakkin mallakar hoto Reuters

'Yan sandan birnin Kabul sun bayyana cewa an kawo karshen musayar wutar da aka yi a otal din Intercontinental, dake babban birnin Afghanistan.

Rundunar 'yan sandan Kasar ta bayyana cewa an kashe duka maharan, sai dai babu tabbaci akan iya adadin wadanda suka rasu.

Kungiyar tsaro ta NATO dai ta bayyana cewa jiragen helikoptoci na kawancen ta sun bude wuta a otal din Intercontinental dake birnin na Kabul, in da Kawancen ya ce harin ya yi sanadiyar mutuwar mayakan sa kai uku, wadanda suka yi ta harbi suma daga kan rufin kwanon otal din.

Wani mai magana da yawun kungiyar tsaro ta NATO Kanal Tim James ya shaidawa BBC cewa wasu daga cikin mayakan sa kan na sanye ne da rigar kunar bakin wake, ta bama bamai.

Mazauna wurin sun bayyana cewa sun razana matuka game da musayar wutar da aka yi ta yi.

Harin da aka kai wa otal din na Intercontinental dai ya biyo bayan dana wasu bama bamai da wasu mayakan sa kai suka yi, wanda Kungiyar Taliban ta ce ita ce ke da alhakin kaiwa.

Kawo yanzu dai babu tabbaci kan iya adadin wadanda suka rasu baya ga mutane hudun da aka tabbatar da rasuwarsu.