Kimanin yara dari takwas daga Somalia ne ke zuwa Kenya

Hakkin mallakar hoto googleimages

Yaki da fari a Somalia ya sa adadin wadanda ke kaura zuwa makwabciyar kasa Kenya karuwa.

Kungiyar agaji ta Save the Children ta bayyana cewa a duk rana akalla yara dari takwas ne kan iso sansanin 'yan gudun hijira dake Dadaab.

Adadin sabbin wadanda ke zuwa sansanin a duk wata ya ninka yanda yake a bara.

Ma'aikatan agaji a sansanin 'yan gudun hijira na Dadaab sun bayyana cewa yaran dake tahowa daga Somalia na zuwa ne likis dasu, kuma a rama, tare da alamun matukar kishirwa.

Kamar dai yadda kungiyar agaji ta Save the Children ta bayyana a kullum, kimanin mutane dubu daya da dori ne ke zuwa sansanin, wanda ya ke a kasar Kenya, kuma a cikin adadin fiye da dari takwas kan kasance yara kanana.

Kungiyar ta kuma ce mafi yawan mutanen na tafiya ne a kafa kafin su iso sansanin.

Shugabar kungiyar agaji ta Save the Children a Somalia Sonia Zambakides ta ce farin ya sa mutane na daukar kasada wajen guduwa sansanin.

Ta dai ce wata mata da ta zo wurin cin abincin su ta ce ta baro yaranta a gida ne a can kauyensu domin ba za ta iya kallar mutuwarsu ba.

Kungiyar ta ce matar ta gudo ne ta baro yaranta shida a gida, biyu dai sun rasu, amma kungiyar ta yi kokarin kaiwa ga sauran hudun.

Tashin hankalin da ke faruwa a Somalia ya tursasa 'yan kasar da dama tsallakowa Kenya, sai dai kuma matsanancin fari da tsadar abinci, ya sanya lamarin ya fi na wanda suka baro muni.

Mai magana da yawun kungiyar Save the Children a nahiyar Afirka Mike Sunderland ya shaidawa BBC yace mafi yawan wadanda suka gudu din, sun taho ne a saboda matsanancin fari.

Mr. Mike dai ya ce abinda ma'aikatan kungiyar Save the children da ke aiki a sansanin 'yan gudun hijira dake Dadaab ke cewa shine kusan duka wadanda suka yi magana da su sun bayyana cewa saboda fari ne suka gudo.

Mr. Mike ya kara da cewa Somalia na fuskantar rikici tun tsawon shekaru da dama, don haka wadanda suka yi nasarar guduwa sun dandana wani yanayi mai muni ne a Somalia kafin su tsallako Kenya

Sansanin 'yan gudun hijira na Dadaab dai shine sansanin da ake ganin shine mafi girma a duniya.

Wuri ne dake karbar bakuncin fiye da mutane dubu dari uku.

Kungiyar agaji ta likiktoci Doctors without boarders ta bayyana cewa mafi yawa daga cikin sabbin zuwa sansanin na matukar bukatar kulawa ta bangaren lafiyarsu.

Ta dai bayyana cewa kimanin rabin adadin yaran da kan isa sansanin ba'a yi musu alluran riga kafi ba.

A yayin da ake ci gaba da tafka rikici a Somalia, da kuma watannin da aka shafe na matsanancin fari, yanayin dake akwai a sansanin wanda a yanzu haka ya cika ya tumbatsa na kara tabarbarewa.

Duk da yunkurin da ake yi na rage yawan mutanen dake sansanonin zuwa wasu wuraren, baya wani tasirin a zo a gani.