Masana na shakka kan matakan tattalin arziki a Najeriya

Masana harkar da ta shafi tattalin arzikin da harkokin diplomasiyya a Najeriya na ci gaba da tofa albarkacin bakin su dangane da alwashin da shugaban kasar Dr Goodluck Jonathan ya dauka, na cewa nan gaba kadan zai bullo da wasu tsauraran matakan tattalin arziki da nufin ciyar da kasar gaba.

Rahotanni sun ambato Shugaban Kasar a lokacin da ya ke kaddamar da wani katafaren kamfani a Jihar Ogun ya na cewa mai yiwuwa sabbin tsauraran matakan tattalin arziki da zai bullo dasu 'yan kasar za su ji a jikin su.

Sai dai ya bukaci Jama'a da su daura damarar tunkarar kalubalen da ke gaban su bayan an bullo da sabbin matakan.

Masana dai na ganin cewa kafin wanna mataki ya dore, har sai in Shugabanni sun nuna cewa su Shugabanni ne, ta hanyar yiwa al'umma aiyukan da suka kamata.