'Boko Haram ba babbar matsala ba ce'

Hakkin mallakar hoto AFP

A Najeriya, Masana harkokin tsaro na ci gaba da zayyana hanyoyin da za a iya bi domin magance matsalar tsaro a Kasar.

Masanan sun mayar da hankali ne musamman a kan tashe-tashen bama-bamai a wadansu jihohin kasar wadanda ake zaton kungiyar Jama'atu Ahlis-Sunnah Lid-Da'awati Wal-Jihad, wadda aka fi sani da suna Boko Haram ke daukar alhakin kaiwa.

Irin wadannan tashe-tashen bama-bamai dai na haddasa asarar rayuka da dukiyoyi da dama.

Masanan dai sun bayyana cewa matsalar Boko Haram ba wata babbar matsala ba ce da za a kasa magance ta.