Dokar takaita zirga-zirga a Abuja

Dokar takaita zirga-zirga a Abuja Hakkin mallakar hoto nema
Image caption An kai hare-haren bam a baya-bayan nan a Abuja

Hukumomi a Najeriya sun kafa dokar takaita zirga-zirga a wuraren shakatawa da sinima da mashayu a Abuja makwanni biyu bayan harin bom din da aka kai a birnin.

Hukumar kula da birnin dai ta ce matakin ya biyo harin bam din da aka kaiwa hedkwatar yansanda a makonni biyun da suka wuce.

A yanzu wajibi ne wadannan wurare su rufe da zarar karfe goma na dare ya yi, yayin da wuraren shakatawar da ke karbar bakuncin yara za su rufe da karfe shida na yamma.

Mutane takwas ne suka rasa rayukansu a lokacin da wani bom ya fashe a hedkwatar 'yan sandan kasar wanda kungiyar Boko Haram ta kai.

An kuma zarge ta da kai harin ranar Lahadi a wata mashaya a garin Maiduguri.

Kungiyar wacce ke kai yawancin hare-harenta a garin Maiduguri a jihar Borno, ta ce tana bukatar kafa tsarin shari'ar musulunci ne, tare da kawar da rashin adalci ta fuskar siyasa.

Tana kuma ikirarin kawar da duk wani tsarin rayuwa na kasashen Yammacin duniya.

"Bukatar tabbatar da tsaro"

An kuma haramta pakin din motoci a wasu hanyoyi dake kusa da sakatariyar ma'aikatun gwamnatin tarayya a birnin.

"Wadannan matakan sun zama wajibi saboda bukatar tabbatar da tsaro domin kare lafiya da dukiyar jama'a," a cewar mai magana da yawun birnin Muhammed Hazat.

Wuraren shakatawa da sinima a birnin na cika makil da mutane idan sun tashi daga aiki ko kuma a ranakun hutu na karshen mako.

Kuma babu shakka wannan hanin zai jefa jama'ar cikin damuwa.

A 'yan kwanakin nan dai hare-haren Boko Haram na karuwa. Kungiyar na amfani ne da babura wajen kai hare-haren.

Malaman addinin Musulunci da na Kirista da 'yan siyasa na daga cikin wadanda hare-haren kungiyar yake ritsa wa da su.