Sojojin Nijeriya zasu gama da Boko Haram

A Najeriya, rundunar Sojin kasar ta ce ta yi amanna cewa za ta iya murkushe Kungiyar Jama`atu Ahlissuna Lidda`awati wal Jihad, wadda aka fi sani da Boko haram, kungiyar da ke ikirarin tashin wasu bama-bamai, da hare-hare a jihar Borno da wasu sassan kasar.

Rundunar ta ce `yan kungiyar ba su da wani karfi fa ce tsorata mutane da suke yi don kada su bai wa jami`an tsaro bayanan da za su taimaka wajen damke su.

Rundunar sojin Nijeriyar ta bayyana haka ne a wani taron manema labarai da ta kira a Abuja.

Kimanin makonni biyu da suka wuce ne, aka kai harin bam a hedkwatar 'yan sandan Nijeriya, a Abuja, harin da ya halaka mutane akala shidda.

Bayan harin, kungiyar ta fito ta bayyana cewa ita ta kai shi, a matsayin martani ga furucin Babban sufeton 'yan sanda Hafiz Ringim dake cewa zasu gama da su.