Girka ta amince da sauye-sauyen tattalin arziki

Girka Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Fira Ministan Girka yana cikin tsaka mai wuya

Majalisar dokokin kasar Girka ta amince da wani shirin tsuke bakin aljihun gwamnati wanda yake haifar da takaddama sosai a kasar.

'Yan majalisa dari da hamsin da biyar ne, daga cikin dari ukku, suka kada kuri'ar yin na'am da matakan baya-bayan nan na rage yawan kudaden da gwamnati ke kashewa. A karkashin sabon shirin za a zaftare fiye da dala miliyan arba'in, daga kasafin kudin kasar ta Girka.

Akwai bukatar majalisar dokokin ta kuma amince da wata sabuwar doka, wadda za ta fayyace yadda za a aiwatar da matakan tsuke bakin aljihun gwamnatin.

An yi artabu

A wajen Majalisar kuma, 'yan sanda sun rika yin artabu da masu zanga-zanga, yayin da 'yan majalisar ke kada kuri'ar.

Kasashe masu amfani da kudin bai daya na Euro, da kuma Asusun bada lamuni na IMF, sune suka bukaci gwamnatin Girkan ta tsuke bakin aljihunta, kamin su sakammata karin kudaden da za su taimaka mata, wajen biyan basussukan da suka yi mata kanta.

Wasu shaidu sun ce wasu masu zanga-zanga sun kutsa kai wani gini na daya ga daga cikin masu baiwa kasar tallafi Eurobank, inda suka yi yunkurin cinna masa wuta.

Sai dai 'yan sandan kwantar da tarzoma sun yi nasarar dakatar da su.