Isra'ila na hana agaji isa Gaza

Gaza Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Wasu masu fafutuka na kiran a 'yanta Zirin Gaza

Wadansu masu fafutuka a kasar Ireland sun zargi Israila da kawo cikas ga wani jirgin ruwan da ke shirin bin sahun ayarin wasu jiragen ruwa zuwa yankin Palasdinu.

Jirgin da kuma mutanen dai na kan hanyarsu ta zuwa Zirin Gaza ne don kalubalantar datsewar da Israila ke yi a yankin.

Masu fafutukar sun ce an lalata farfelar jirgin nasu ne yayin da suka ya da da zango a kasar Turkiyya.

A makon jiya ma an lalata wani jirgin ruwan kasar Sweden wanda ke shirin shiga ayarin jiragen da ke kan hanyarsu ta zuwa Palasdinu

A bara ma sojojin kundumbala na Isra'ila sun kutsa kai cikin jirgin ruwan Turkiyya wanda ke gab da isa yankin na Gaza, inda suka kashe masu fafutukar kwato 'yancin Palasdinu da dama.

An yi Allah wadai da Isra'ila

Lamarin dai ya haifar da baraka tsakanin dangantakar Isra'ila da Turkiyya - wacce ita ce kasar musulunci ta farko da ta amince da Isra'ila a matsayin kasa.

Kungiyoyin kare hakkin bil adama daga sassa daban daban na duniya sun yi Allah wadai da matakin Isra'ila na datse yankin na Gaza.

Kungiyoyin dai na cewa matakin ya jefa rayuwar Palasdinawa cikin mawuyacin hali.

A 'yan kwanakin nan ma Majalisar Dinkin Duniya ta ce yankin na Gaza na daga cikin yankunan da suka fi fama da rashin aikin yi a duniya.