An yi wajirgin ruwan kasar Ireland kafar ungulun zuwa Gaza

Wasu masu fafutuka a jamhuriyar Ireland sun zargi Israila da kawo cikas ga wani jirgin ruwan dake shirin bin sahun ayarin wasu jiragen ruwa dake hanyarsu ta zuwa Gaza don kalubalantar datsewar da israila ke yi wa yankin Palasdinu.

Masu fafutukar, sunce an lalata farfelar jirgin na su ne yayinda suka yada zango a Turkiyya.

A makon jiya ma an lalata wani jirgin ruwan kasar Sweden dake shirin shiga ayarin jiragen da ke hanyarsu ta zuwa Palasdinun.