Sammaci kan wasu jami'an Lebanon

Rafik Hariri Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Ana yi wa Rafik Hariri kallon mutumin da ya dora Lebanon kan tafarki

Babban mai shigar da kara na Lebanon ya ce kotun duniya da ke binciken kisan tsohon Fira Ministan kasar Rafik Hariri ta bada da sammacin kame mutane hudu.

Dan Mr Hariri, Saad, ya yi maraba da sammacin yana mai cewa "ba za a manta da shi" a tarihin kasar ba.

Rahotanni daga kasar sun ce sammacin ya shafi wasu daga cikin manyan jami'an kungiyar 'yan Shi'a ta Hezbollah.

Hezbollah ta yi watsi da kotun sannan ta yi alkawarin mayar da martani.

An kashe Rafik Hariri tare da wasu mutane 21 a watan Fabrerun 2005 a tsakiyar birnin Beirut lokacin da wani shirgegen bom ya tashi yayin da motocinsa ke giftawa.

Hezbollah ta zargi kotun sannan ta yi yunkurin bata mata suna, tana mai cewa wata makarkashiya ce ta Amurka da Isra'ila da kuma Faransa.

Kungiyar ta kuma musanta batun hannu a kisan.