An yi kiran raba Najeriya

Taswirar Najeriya
Image caption Ga alama sabuwar Najeriya ba za ta hada da jihohin shari'a

A Nijeriya, wasu kungiyoyi da suka fito daga kudancin Naijeriya da wadanda suka fito daga yankin tsakiyar Nijeriya, wato Middle Belt sun yi kiran da a samar da wata sabuwar Naijeriya, wadda zata samar masu da abin da suka kira kyakkyawar makoma.

Kungoyin sun yi korafin cewa kundin tsarin mulkin Naijeriya na 1999 ba shi da wani tasiri ga al'ummar kasar.

Sun bayyana haka ne a wani taron manema labaru da wata kungiyar ta sabuwar Nijeriya ta kira, domin nazari kan rikicin da ya biyo bayan zabe a Nijeriya.

Taron ya zo ne a karkashin kungiyoyi uku, wato kungiyar al'ummar yankin Naija-Delta, kungiyar Yarbawa da Igbo da kuma kungiyar yankin tsakiyar Najeriya.