An kashe mutane dayawa a Afghanistan ciki har da wakilin BBC

Ahmad Omid Khpolwak, wakilin BBC da aka kashe a Afghanistan Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Ahmad Omid Khpolwak, wakilin BBC da aka kashe a Afghanistan

Sama da mutane 20 ne suka hallaka, cikinsu har da wani wakilin BBC, a hare-haren da 'yan gwagwarmaya suka kai a kudancin Afghanistan.

Masu tada kayar bayar sun kai hare haren kunar bakin wake uku a Tarin Kot, babban birnin lardin Uruzgan.

Daya daga cikin bama-baman ya tashi a wajen ofishin gwamnan lardin, yayin da wani kuma ya tashi a wani kamfanin aikin gadi dake karkashin wani babban kwamanda a lardin.

Bayan fashewar bama-baman sai aka rika kazamar musayar wuta tsakanin dakarun tsaro da masu tada kayar bayan a babbar kasuwar garin.

Wakilin BBC, Ahmad Omid, mai shekaru 25 a duniya, yana daga cikin wadanda suka rasa rayukansu.

Ya yi shekaru uku ya na aikowa sashin Pashto na BBC rahotanni, kuma ya na aiki da kamfanin dillancin labarai na Pajhwoke, sannan kuma yana gabatar da wani shiri a wani gidan radiyo a kasar.

Rahotanni sun ce yana aiki ne a gidan talabijin da rediyo na lardin a lokacin da 'yan bindigar suka kai hari.