Najeriya na korar 'yan kasashen waje

Taswirar Najeriya
Image caption Taswirar Najeriya

Hukumomin Nijar sun tabbatar da cewa, an koro 'yan kasar su fiye da 130 daga Najeriya.

Hukumomin shige da fice na Najeriyar ne suka dauki matakin korar mutanen da suka hada da wasu 'yan kasashen dabam, bisa zargin rashin mallakar cikakkun takardun zama a Najeriyar.

Tun a bara ne hukumomin Najeriyar suka ba 'yan kasashen wajen da ke zauna a kasar wa'adin su yi rajista, idan ba haka ba kwa a kore su daga kasar.

Kawo yanzu 'yan kasashen wajen da ke zaune a jihohin Kwara da Osun ne jami'an shige da ficen suka tasa keyarsu zuwa gida.

Wasu kungiyoyin kare hakkin jama'a a Nijar sun koka da wannan matakin da Najeriyar ke dauka.

Hakan na faruwa a daidai lokacin da 'yan Nijar fiye da dubu 200 suka koma kasar daga Libiya, sakamakon tashin hankalin da ake yi a can.