Agajin kusurwar gabashin Afirka mai fama da yunwa

Kusurwar gabashin Afirka
Image caption Kusurwar gabashin Afirka

Babban kwamishinan hukumar kula da 'yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya, Antonio Gutteres, ya yi gargadi game da girman matsalar tamowa a tsakanin kananan yaran da ake gudun hijira da su, domin tsere wa matsalar fari a Somaliya.

A cewar kwamishinan, matsalar tana kara kamari, kuma zata haddasa mace macen da zasu sha gaban duk wani tunanin dan adam.

Hukumar kula da 'yan gudun hijirar ta ce, ana matukar bukatar agaji cikin gaggawa na abinci, da wuraren kwana da ababen kiwon lafiya, da ma sauran abubuwa na ceto rayuka.

Kiran na mista Gutteres ya zo a daidai lokacin da kungiyoyin bayar da agaji na Birtaniya, irinsu Oxfam da Save the Children da kuma Red Cross, su ka kaddamar da neman taimakon gaggawa don tinkarar matsalar abincin da ke shafar mutane fiye da miliyan 12, a kusurwar gabacin Afrika.