Shekaru 20 da shirya babban taron kasa a Nijar

Taswirar Nijar Hakkin mallakar hoto bbc
Image caption Taswirar Nijar

A jamhuriyar Nijar yau ake bukukuwan cikar shekaru 20 da shirya babban taron kasa, wato Conference Nationale, wanda ya dora kasar a kan tafarkin demokradiyya.

Taron ya bude hanyar kafa jam'iyyu da dama a kasar ta Nijar, wadda kamin lokacin ta kwashe shekaru da dama a karkashin mulkin soja.

Sai dai a daidai lokacin da wasu 'yan kasar ke ganin wannan mahawarar ta yi abin a zo a gani , wasu na cewa har yanzu akwai bukatar gyara ga tsarin demokradiyya a kasar.

Hukumomin sun shirya biki a birnin Yamai, domin tunawa da ranar da aka bude taron, shekaru ashirin da suka gabata.