Almundahna a ma'aikatun shari'ar Nijar

Taswirar Nijar Hakkin mallakar hoto bbc
Image caption Taswirar Nijar

Gwamnatin Nijar ta ce, ta gano wasu laifufukan almundahna 23 da aka tafka a cikin wasu ma'aikatun shari'a na kasar.

Ministan shari'a, kuma kakakin gwamnati, Malam Marou Amadou, shi ne ya tabbatar da hakan, a lokacin taron majalisar ministocin kasar da aka yi a jiya.

Sai dai wasu kungiyoyin kare hakkin dan adam na ganin akwai bukatar gwamnatin ta fito fili ta yi wa 'yan kasar bayani, a kan mutanen da ke da hannu a cikin almundahnar, da kuma adadin kudaden da suka salwanta.

Tun da ya hau kan karagar mulki a farkon watan Afrilu, shugaban kasar ta Nijar, Alhaji Issoufou Mahammadou, ya yi alkawarin shawo kan matsalar cin hanci da karbar rashawa.