Jana'iza a kasar Norway

Jana'iza a kasar Norway Hakkin mallakar hoto r
Image caption Jana'iza a kasar Norway

Shugabannin siyasa da sauran jama'ar Norway na halartar jana'izar mutane 76 da aka kashe a ranar juma'ar da ta gabata.

Yawancin wadanda aka kashe din dai yara ne da basu kai shekaru ashirin ba, a hare haren da aka kai yau mako guda cif kenan.

Wanda ya dauki alhakin kashe kashen, Anders Breivik, an dauke shi daga kurkuku zuwa wani ofishin 'yan sanda domin yi masa tambayoyi.

An ce kuma kwararru na bincike kan hankalinsa.

Kisan na kan mai uwa da wabi da wannan mai tsatsauran ra'ayin ya aikata, ya shafi jama'a da dama, ciki kuwa har da 'yan kasashen waje wadanda suka yi gudun hijira domin neman mafaka a kasar ta Norway.

A sassa daban daban na kasar an sabko da tutoci kasa-kasa, domin yin juyayi da tunawa da wadanda suka rasa rayukan nasu.