Shakku na bayyana a shari'ar Strauss-Kahn

Dominique Strauss-Kahn Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Tsohon shugaban IMF, Dominique Strauss-Kahn

Ga alamu shari'ar da ake yiwa tsohon shugaban Asusun ba da Lamuni na Duniya (IMF), Dominique Strauss-Kahn, na fuskantar matsala yayin da ake samun rahotannin da ake nuna shakku a kan gaskiyar matar da ta zarge shi.

Jami'an tsaro sun shaidawa kafofin yada labarai na Amurka cewa matar ta yi ta sharara karya tun bayan da ta zargi Mista Strauss-Kahn a watan Mayu.

Jami'ai sun ce ga alama matar, wadda haifaffiyar kasar Guinea ce, ta yi karya yayin da ta ke cike takardun neman mafaka a Amurka.

Ranar Juma'a ne dai ake sa ran Mista Strauss-Kahn ya bayyana a gaban kotu, kuma lauyoyinsa za su nemi a sassauta ka'idojin da aka gindaya kafin a ba shi beli.

An yiwa dan siyasar na kasar Faransa mai shekaru sittin da biyu da haihuwa daurin talala ne a wani gida a birnin New York, inda masu gadi dauke da makamai da kuma na'urori ke sanya ido a kansa, bayan da aka bayar da belinsa a kan tsabar kudi dala miliyan shida a watan Mayu.

An dai tuhumi Mista Strauss-Kahn ne da tuhume-tuhume guda bakwai da suka danganci yunkurin yin fyade.

Sai dai Mista Strauss-Kahn, wanda ya ajiye aikinsa na shugabancin IMF don ya kare kansa, ya musanta tuhume-tuhumen.

A lokutan zaman kotu a baya dai masu shigar da kara sun nuna cewa suna da kwararan hujjoji.

Sai dai a halin yanzu kafofin yada labarai na Amurka sun bayar da rahoton cewa masu shigar da karar na shirin bayyana damuwarsu dangane da gaskiyar ma'aikaciyar otal din da ta zargi Mista Strauss-Kahn ga lakali ranr Juma'a.

Jaridar New York Times ta ruwaito cewa ko da ya ke binciken kwakwaf ya gano shaidar cewa ba ko tanatama Mista Strauss-Kahn ya sadu da matar, masy shigar da karar sun ce yanzu suna shakkar bayanan da matar ta yi musu a kan kanta da kuma dangane da yanayin saduwar.

A cewar jaridar, masu shigar da karar sun yi imanin cewa akwai bayanai masu karo da juna a takardun matar na neman mafaka a Amurka.

Matar dai ta shaidawa hukumomi ne cewa Mista Strauss-Kahn ya nemi ya yi lalata da ita lokacin da ta shiga dakinsa a otal din Sofitel da ke New York don ta share dakin.

A da dai ana sa ran lauyoyin da ke kare Mista Strauss-Kahn za su kafa hujja cewa ya sadu da matar amma bisa amincewarta.

Kafin wannan zargi ya bayyana dai ana yiwa Mista Strauss-kahn kallon na kan gaba a cikin masu son tsayawa takarar shugabancin ksar Faransa a bangaren masu matsakaicin ra'ayin gurguzu.

Tsohon Firayim Minista Lionel Jospin mai ra'ayin gurguzu ya kwatanta bayanan da suka fito na baya-bayan nan da tsawa.

Da ya ke suka a fakaice kan tsarin shari'a na Amurka, Mista Jospin ya ce "Abin da aka yiwa [mista Strauss-Kahn] kare ba ya ci ba".