Za a gudanar da bincike kan hukumar CIA

Za a gudanar da bicike kan CIA Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Eric Holder

Hukumomi a Amurka sun ce za su fara gudanar da bincike kan zargin da ake yiwa hukumar leken asiri ta CIA dangane da mutuwar wasu masu zaman gidan-yari a kasashen waje.

Babban lauyan gwamnatin Amurka, Eric Holder, ya ce sun shafe shekara biyu da rabi suna tattara bayanai, inda suka samu shaidu da za su wadatar wajen yin cikakken bincike a kan batun.

Batu na farko dai da binciken zai duba shi ne na kisan wani mai suna Gul Rahman, wanda ya mutu a gidan-kaso a birnin Kabul a shekara ta 2002.

Sau da yawa ana zargin hukumomin tsaron Amurka da musgunawa jama'ar kasashen da aka kai su don tabbatar da tsaronsu.