An yi wa shugaba Chavez tiyata

Shugaba Hugo Chavez Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Shugaba Hugo Chavez na jinya a kasar Cuba

Shugaban Sojan Venezuela ya yi watsi da damuwar da ake nunawa game da rashin Shugaba Hugo Chavez a kasar.

Shugaban sojin, Janar Henry Rangel Siva, ya ce har yanzu shugaban ne ke tafiyar da harkokin kasar, kuma babu wata barazana ga tanadin tsarin mulkinta.

Ya kara da cewar Mr Chavez na murmurewa yadda ya kamata, kuma nan ba da jimawa ba zai koma gida.

Tun farko Shugaban na Venezuela, Hugo Chavez ya ce aamsa cewar an yi masa aikin tiyata, saboda cutar daji abunda ya kawo karshen shaci fadin da akeyi akan abunda ya sa ya jima a Cuba.

Shugaba Chavez ya aikewa 'yan kasarsa sako ta gidan telbijin daga Havana Babban birnin kasar cuba, inda yace yana samun sauki.

Ya ce, " tiyata ce aka yi sosai, amma kuma komai ya tafi dadai kuma ina ci gaba da murmurewa. Yanzu dai ina shan magunguna".

Ba a dai san irin halin da Chavez ya ke ciki ba,amma 'yan adawa sun nuna shakku kan yadda zai iya yin mulki kasar daga waje.