Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Haifi Ki Yaye da BBC Hausa: Shayar da jarirai nonon uwa

Hakkin mallakar hoto google
Image caption Ana takadda kan lokacin da ya kamata a fara baiwa jariri abinci mai nauyi

A cewar hukumar lafiya ta duniya, samun abinci mai gina jiki na da muhimmancin gaske ga rayuwar dan adam, kama daga abinda ya shafi girmansa da bunkasar kwakwalwarsa da kazar-kazar da kuma koshin lafiyarsa a fadin rayuwarsa.

Tun yana dan tayi a cikin mahaifiyarsa da gurin haihuwarsa da sanda ya ke jariri zuwa kuruciya ya zuwa lokacin da ya mallaki hankalinsa.

Shayarwa wato bayar da nonon uwa shi ne mataki na farko acewar hukumar na samun abinci mai gina jiki ga jariri bayan haihuwarsa domin ya kunshi dukkan sinadaren da ake bukata wajen girma cikin koshin lafiya.

Haka kuma hukumar ta bayyana cewa kusan dukkan uwa za ta iya shayar da jariri ko jaririyarta, muddin ta samu cikakken bayanin yadda ya kamata ta yi hakan da kuma kwarin guiwa daga iyalanta da tsarin kiwon lafiya da kuma al'umma baki daya.

Inda hukumar ta bada shawarar shayar da yara nonon uwa zalla a watanni shida da haihuwarsu kafin a fara hada musu da wani abinci. To ko ta yaya yakamata mace ta shayar da jaririnta? Shrin Haifi Ki yaye da BBC Hausa na wannan makon ya amsa wannan tambaya.