Strauss-Kahn zai koma harkokin siyasar Faransa

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Mista Strauss-Kahn

A Faransa, ana hasashen cewa mai yiwuwa tsohon shugaban Hukumar Ba da Lamuni ta Duniya, Dominique Strauss-Kahn, ya sake shiga fagen siyasar kasar.

Hakan na faruwa ne bayan kotu ta sake shi daga daurin talalar da ta yi masa, kan zargin yunkurin yin lalata da wata ma'aikaciyar wani Otel a Amurka.

Amma alkali ya ce sakin da aka yiwa Mista Strauss-Kahn ba wai yana nufin maganar ta mutu ba ne, don an sake shi ne yayin da ake ci gaba da shari'ar.

Lauyan da ke kare Mista Strauss-Kahn ya ce dama zargin da ake yi masa ba shi da tushe, domin tun da farko ba su amince da zargin ba.

Shi ma lauyan da ke kare matar ya ce zai yiwu alkali ya yi watsi da karar.

Shi dai Mista Strauss-Kahn na da matukar tasiri a siyasar Faransa kafin kamun da aka yi masa, kuma sakinsa na yin barazana da Shugaba Nicholas Sarkozy, wanda ke neman sake darewa karagar mulkin kasar.