Jami'an tsaro a Nijeriya sun kama Malam Nasir Elrufa'i

Malam Nasir Elrufa'i
Image caption Malam Nasir Elrufa'i

Rahotanni daga Nijeriya sun ce jami'an tsaro na SSS sun tsare tsohon ministan babban birnin Tarayya Abuja, Malam Nasir Elrufa'i.

Rahotannin suka ce jami'an tsaron sun tafi da shi ne bayan ya sauka a filin jirgin sama na Abuja.

Malam el-Rufai dai ya rubuta sakwannin twitter wadanda a ciki ya ba da labarin cewa ya isa hedkwatar SSS din kuma an haura da shi ofishin daraktan hukumar.

Hukumar ta SSS ta ce ya zama wajibi ta kama Malam El-Rufai ne saboda kalaman da ya ke wallafawa a intanet da jaridu wadanda ta ce za su ta da zaune tsaye.

Tuni dai dantakarar shugabancin Najeriyar a karkashin tutar jam'iyyar CPC, Janar Muhammadu Buhari, ya yi Allah wadai da kama tsohon ministan.