Shugaba Jonathan ya rantsar da ministoci a Nijeriya

Shugaba Goodluck Jonathan Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Shugaba Goodluck Jonathan

A Najeriya, an rantsar da kashin farko na ministocin da majalisar dattawan kasar ta tantance, daga cikin wadanda shugaba Goodluck Jonathan ya mika mata.

Wadanda aka rantsar din dai su goma sha hudu ne, kuma sha biyu daga cikinsu tsoffafin `yan majalisar zartarwar kasar ne da aka rusa kwanan nan.