Shugaban Syria ya kori Gwamnan Hama

Masu zanga zanga a Syria Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Masu zanga zanga a Syria

Shugaban kasar Syria Bashar Al 'asad ya kori gwamnan birnin Hama, Ahmad Abdulaziz Khaled.

Ana ganin shugaban kasar ya dauki wannan matakin ne saboda rikicin da ya barke a birnin a farkon watan da ya gabata, lokacin da aka kashe akalla mutane tamanin.

Watanni uku bayan fara wannan bore gwamnati na ta kokarin shawo kan wannan rikici na Syria.