ACN ta gano kura-kurai a dokokin zaben Najeriya

Image caption Tambarin jam'iyyar ACN

A Najeriya, jam'iyyar adawa ta ACN ta ce ta gano kura-kurai da dama da ta ce an tafka a gyare-gyaren da Majalisar Dokoki ta kasa ta yiwa kundin dokokin zabe.

Sakataren jam'iyyar Sanata Lawal Shu'aibu, ya shaidawa BBC cewa za su sanar da duniya irin kura-kuran da Majalisar ta yi, sannan su bukaci ta gyara su, idan ba haka ba su kaita gaban kotu.

Sai dai Majalisar Dokokin ta ce ta yi iya bakin kokarinta, don haka ya rage ga kotunan kasar su yi fassarar abin da ta yi, sannan su amince da shi ko su yi watsi da shi.

Ko a karshen makon da ya gabata ma sai da wata kotu ta soke ayar doka guda daga cikin gyare-gyaren da Majalisar Dokokin ta yiwa kundin dokokin zaben.