Jami'an tsaron Nijeriya sun saki el-Rufa'i

Malam Nasir el-Rufa'i
Image caption Malam Nasir el-Rufa'i

Jami'an tsaro na farin kaya a Najeriya, wato SSS, sun saki Malam Nasir el- Rufa'i, wanda suka kama jiya bisa zargin rubuce-rubucen da suka yi zargin za su iya tayar da hankali.

Jami'an tsaron sun ce an tsare Malam el-Rufa'i ne saboda wani rubutu da ya yi a wata jarida wanda a ciki ya ce ba wasu ayyuka masu inganci da gwamnatin ke aiwatarwa, ga kuma makudan kudaden da ta ke kashewa.

Sun kuma bayyana cewa rubutun da el-Rufa'i ya yi zai iya harzuka jama'a, sannan ya tayar da zaune tsaye.

Jami'an su ka ce Malam el-Rufa'i bai yi bincike game da bayanan da ya rubuta ba.