'Yan bindiga sun harbe magidanta a Maiduguri

Jami'an 'yan sandan Nijeriya
Image caption Jami'an 'yan sandan Nijeriya

Rahotanni daga jihar Borno a Najeriya sun tabbatar da cewa wadansu 'yan bindiga sun shiga gidaje daban daban a tsakiyar birnin Maiduguri, inda suka kashe wasu magidanta da ma karin wasu jama'ar.

Da misalin karfe goma sha daya zuwa sha biyun daren jiya Asabar ne dai al'amarin ya faru a gidaje uku da ke unguwar Bulabulum Garnam.

A gida na farko dai 'yan bindigar sun haura ta katanga ne sannan suka harbe maigidan; a gida na biyu kuma wa da kani aka harbe.

Har yanzu dai jami'an tsaro ba su yi bayanin yawan wadanda suka rasa rayukansu, amma dai 'yan sanda sun ce suna zargin wadanda suka saba kai hare-hare da kai hare-haren na baya-bayan nan.

Hakan dai ya faru ne a wani lokaci da jama'a ke zaune cikin zullumi sakamakon hare-hare da tashe tashen hankulan da ake fama da su a jihar.

Jami'an tsaro a birnin na Maiduguri sun tsare wadansu mutane bisa zargin hannu a wannan al'amari, kuma suna ci gaba da gudanar da bincike.