Jamhuriyar Nijer ta dakatar da huldar kasuwanci da Libya

Shugaban kasar Nijer Muhammadou Issoufou
Image caption Shugaban kasar Nijer Muhammadou Issoufou

A jamhuriyar Nijer shugaban kasar Alhaji Muhammadou Issoufou ya ce Niger ta dakatar da huldar kasuwanci da makwabciyarta Libya, sakkamakon yakin da ake yi a kasar.

Har ila yau, shugaba Muhammadou Isoufou ya ce yanzu haka kimanin mutane dubu dari biyu da goma sha daya ne suka kwararo kasar ta Niger tun bayan barkewar yakin a Libya, abin da ya ce yana yi wa kassar ta Nijer barazana ta fannin tsaro.

Shugaban Nijer din ya bayyanawa manema labarai hakan ne jiya da daddare a lokacin da ya dawo gida daga taron koli na kungiyar Tarayyar Afirka wato AU da akai a kasar Equatorial Guinea.