'Yan adawa na shirin kafa gwamnati a Thailand

Zabe a Thailand Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Zabe a Thailand

Sakamakon wucin gadi na zaben da aka gudanar a kasar Thailand ya nuna cewa jam'iyyar adawa wacce take da alaka da tsohon Firayim Ministan kasar, Thaksin Shinawatra, tana kan hanyar lashen zaben da gagarumin rinjaye.

'Yar uwar Mista Thaksin din, Yingluck, ita ce take jagorantar bangaren adawar.

Tana kuma kan hanyarta ta zama Firayim Minista mace ta farko a kasar ta Thailand.

Yingluck, da kuma Firaminista mai ci yanzu, Abhisit Vejjajiva, sun yi yakin neman zabe ne bisa bukatar hadin kan kasar bayan shekaru na rarrabuwar kai.