Yau ake gudanar da zaben shugaban kasa a Thailand

Image caption Abhisit Vejjajiva

Al'ummar kasar Thailand na kada kuri'a a zaben kasa baki daya da ake gudanarwa a yau Lahadi.

Zaben dai na zuwa ne bayan fadi-tashin siyasa da kasar ta fuskanta cikin shekaru biyar din da suka gabata.

Miss Yingluck Shinawatra, kanwar tsohon shugaban kasar Thaksin Shinawatra, na kalubalantar Firayim Minista, Abhisit Vejjajiva.

Shi dai tsohon shugaban kasar na gudun hijira a Dubai bayan da hukumomi suka zarge shi da cin-hanci.

Sai dai yana da matukar farin-jini a kasar sakamakon ayyukan ci gaban da ya aiwatar.