Tsugunne bata karewa DSK ba

Dominique Strauss Kahn Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Dominique Strauss Kahn

Akwai yiwuwar tsohon shugaban asusun bada lamunin IMF, Dominique Strauss Kahn, zai sake gurfana a gaban kotu, idan kotun New York ta sake shi, sai dai a wanan karon a Faransa.

Wata marubuciya ce, Tristane Banon, ta yi ikirarin cewa ya afka ma ta a 2002.

Lauyanta, David Koubbi, ya ce lamarin na da nasaba ne da wani abun da ya faru, lokacin da ta je yin hira da Mr Strauss Kahn a gidansa dake birnin Paris.

Lauyan ya ce, za ta shigar da kara a gobe Talata, bisa zargin kokarin yi mata fyade.

A ranar Juma'a ce aka bada belin tsohon shugaban hukumar ta IMF din, daga daurin talala mai tsauraran ka'idojin da aka yi masa.

Masu gabatar da kara ne suka bukaci hakan, bayan da suka fara nuna shakku game da sahihancin wadda ke zargin nasa, wadda kuma ita ce babbar shaidarsu.