Wasu mutane sun arce da albashin ma'aikata

Rahotanni daga jihar Borno a arewacin Najeriya na nuna cewar kimanin mutane hudu ne ciki har da jami'in tsaro, suka rasu sakamakon harin da wasu da ake zargin 'yan fashi da makami ne suka kai kan wata mota, dauke da albashin ma'aikata.

Ana zargin cewa maharan sun bude wuta kan jami'an ne, a kan hanyarsu ta zuwa karamar hukumar Shani, suka kuma yi awon gaba da kudaden.

Jihar Borno dai na daga cikin jihohin Nijeriya da suka fi fama da barazanar tsaro da ta hada da hare haren 'yan kungiyar jama'ati ahlil sunna li da'awati wal jihad, da aka fi sani da suna Boko Haram, da kuma na 'yan fashi da makami.

Ko a 'yan kwanakin da suka wuce, an kai hare hare da dama da suka haddasa asarar rayukan jama'a.