'White House' makasar jama'a a kudancin Sudan

Kudancin Sudan Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Kimanin mutane 1,800 ne suka mutu a fada tsakanin Kudanci da Arewacin Sudan

Wani gida da ake kira "White House" a birnin Juba na daga cikin wuraren da ke matukar firgita jama'a saboda ana hallaka jama'a a wurin, musamman wadanda ake zargin cewa 'yan tawaye ne.

Wakilin BBC ya ziyarci wani dan karamin daki a gidan wanda hayaki ya maida bangonsa bakikkirin, baya ga tarin kasar da aka zuba a buhuhuna.

Wani mutum a wurin ya shaida wa BBC cewa ana amfani da buhuhunan ne wajen azabtar da mutanen da aka kama daga Kudancin Sudan ko kuma 'ya'yan kungiyar tawaye ta SPLA.

Irin wadannan gine-gine, ba kawai suna tunatar da irin mummunar zubar da jinin da aka yi a Kudancin Sudan ba ne, mutane na ganinsu a matsayin darasi ga al'umma masu tasowa.

"Wurin na tuna mana da bala'in da muka fuskanta , idan ka samu labarin cewa an tafi da wani can to shi ke nan domin ba a dawowa," a cewar wani dalibin kwaleji mai suna Mabil William.

Ba a kara jin duriyar mahaifinsa ba bayan kama shi da akayi a lokacin yaki, kuma ana tunanin ya mutu ne a White House. "Lokacin da na kada kuri'ar neman ballewa daga khartoum, irin wadancan wurare nake kokarin gujewa."

Sai dai yayinda mutane ke cike da fata mai yawa, akwai kuma kalubale da dama.

Kungiyar SPLA wacce ke jagorantar Kudancin Sudan ba ta da tarihi mai kyau.

Rikidewar da ta yi daga kungiyar 'yan tawaye zuwa rundunar soji ya haifar da zargin cin zarafi da kisan jama'a daga kungiyoyin kare hakkin bil'adama.

"Rahoto na baya-bayan nan ya yi zargin aikata munanan kashe-kashe, da muzgunawa fararen hula da wawure dukiyar jama'a", a cewar rahoton hadin gwiwa na kungiyoyin kare hakkin bil'adama na ciki da wajen Sudan.

Sun yi gargadin samun wata "gwamnatin kama-karya a Kudancin Sudan, inda iko da kudi zai kasance a birnin Juba kacal, sannan batun tsaro ya lashe mafi yawan kasafin kudin kasar.

Makabarta

Sojojin Arewaci Sudan sun bar White House, amma har yanzu yankin na karkashin soji bayan da aka maida shi barikin soji karkashin ikon SPLA.

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Akwai babban kalubale a gasan Sylva Kiir da mataimakansa

Akan dauki fursunoni zuwa wurin domin azabtar da su - koma a hallaka su.

A yanzu a kan yi amfani da ginin ne wajen ajiye kayayyaki da kuma makwanci.

Manjo Janar Marial Chanoung, kwamandan da ke kula da wurin, ya ce babu tabbas kan dubban 'yan Kudancin da suka mutu a wurin.

"An ci zarafin jama'a. Wuri ne da aka yi imanin cewa an kashe mutane da dama," a cewarsa.

Sai dai Manjo Gen Chanoung na ganin ba zai yiwu a maimaita wannan mummunna aiki ba.

"Dole a dakatar da maganar White House nan gaba a Kudancin Sudan, kai ba zai yiwu ba kwata-kwata."

Karin bayani