Kalubalen dake gaban Sudan ta Kudu

kudancin Sudan
Image caption 'Yan kudancin Sudan na murna bayan kuri'ar raba-gardama a London

Tun kafin Kudancin Sudan ta zamo kasa mai cin gashin kanta, tuni take fafata yaki da kusan kungiyoyin 'yan tawaye bakwai da ke yankin.

Wani faifen bidiyo da BBC ta samu, ya nuna daruruwan mayakan 'yan tawaye suna daga sabbin makamansu da nuna yunkurin kai farmaki.

'Yan tawayen sun sha gwabza kazamin fada da sojojin Kudancin Sudan, abin da ke nuna irin kalubalen da ke gaban sabuwar kasar.

Wani abu da ke karawa 'yan tawayen kwarin gwiwa shi ne kasancewar shugabanninsu tsaffin kwamandojin Sudan People's Liberation Army (SPLA) ne, ko kuma kungiyoyin da suka yi yaki da gwamnatin Sudan a shekaru 21 da aka shafe ana gwabza yaki.

An kawo karshen yakin ne sakamakon yarjejeniyar zaman lafiyar da aka cimma wacce ta share hanyar samun 'yanci ga Kudancin Sudan.

Daya daga cikin kungiyoyin 'yan tawayen, South Sudan Liberation Army (SSLA) ta Peter Gadet , ta ce tana yakar cin hanci da rashawa ne, da kuma mamayar da 'yan kabilar Dinka suka yi a kasar.

Ana zargin 'yan kabilar ta Dinka da mamaye manyan mukamai a rundunar sojin yankin da kuma gwamnati.

Kudaden da ake kashewa a kan kungiyar SPLA sun haura kashi 25 cikin dari na kasafin kudin Kudancin Sudan, kuma ya ninka sau uku kudaden da ake kashewa kan fannin lafiya da ilimi.

Wannan dai na nuna yadda gwamnatin ta ke maida martani ga barazanar 'yan tawayen da kuma tsaffin abokan adawarta da ke birnin Khartoum.

Sai dai mafi yawan kudin na tafiya ne wajen biyan albashi, kuma babban jami'in Majalisar Dinkin Duniya a Kudancin Sudan David Gressley, ya yi kira da a rage sojojin kasar bayan an samu 'yancin kai.

Arewacin Sudan

Kungiyar SSLA ta sha fafatawa da SPLA, a kusa da sansanin da ta fi karfi a Unity state.

A cewar SPLA, kungiyar na samun goyon baya ne da kuma tallafin makamai daga Khartoum.

BBC ta samu faifen bidiyon ne daga hannun wani shugaban 'yan tawayen wanda ke zaman wucin gadi a birnin Khartoum.

Kungiyoyin 'yan tawayen da ke yakar mahukunta a Kudancin Sudan, sun kai kusan bakwai.

Ko ta wanne hali dai, Juba na ganin akwai hannun Khartoum a bore na bayan-bayan nan, kuma hakan na da tasiri sosai a dangantakar da ke tsakaninsu.

A lokacin yakin basasar da aka shafe shekaru ana yi, arewacin Sudan sun yi amfani da kudi wajen raunana kungiyar SPLA.

Koda mataimakin shugaban kasa na Kudancin Sudan Riek Machar, ya taba bijirewa daga kungiyar ta SPLA. Shugaba Omar al-Bashir na National Congress Party (NCP), ya musanta cewa suna goyon bayan sabbin kungiyoyin 'yan tawayen na Kudancin Sudan.