Masu zanga zanga sun kara da jami'an tsaro a Hama

Rahotanni daga Birnin Hama na Syria sunce ana dauki ba dadi kan tituna tsakanin dakarun tsaro da masu zanga zanga, kwana 3 bayan wata gagarumar zanga zangar kin jinin gwamnati.

Mazauna birnin sunce da safiyar yau yansanda da sojoji dauke da makamai sun shiga birnin sun kama mutane akalla 20.

Daga nan Kungiyoyin matasa sun hau kan tituna suka tinkari dakarun tsaron , suna jefa da duwatsu da kuma kakkafa shingaye kan hanyoyi.

A halin yanzu ance tankokin yaki da kuma sauran motocin sojin da suka zagaye birnin na Hama a jiya lahadi sun kama gabansu, kuma sun doshi arewa zuwa lardin Idlib.