Turkiya ta bayyana goyon bayanta ga 'yan tawayen Libya

Image caption Ministan Harkokin Wajen Turkiya, Ahmed Davutoglu

Kasar Turkiya ta bayyana goyon bayanta ga 'yan tawayen kasar Libya wadanda ta ce su ne halastattun jagororin al'ummar kasar.

Ministan Harkokin Kasashen Wajen Turkiya Ahmed Davutoglu ne ya bayyana hakan ranar Lahadi a lokacin da ya kai ziyara ga 'yan tawayen a birnin Beghazi da ke gabashin kasar.

Ya ce Turkiya za ta taimakawa 'yan tawayen Libya da kudi kimanin dala miliyan dari biyu domin su ci gaba da fafutikar da suke yi ta ganin sun kawar da Shugaba Mu'ammar Gaddafi daga mulki.

Wannan sanarwa na zuwa ne kwana daya bayan da 'yan tawayen suka bayyana shirinsu na fadada hare-haren da suke kaiwa inda za su nufi birnin Turabulus.

A bangare guda, Shugaban kasar Rasha, da takwaransa na Afirka Ta Kudu, da kuma Babban Sakataren Kungiyar NATO za su tattauna kan rikicin da ake yi a kasar Libya.

Za su gudanar da tattaunawar ne a kasar Rasha a yau Litinin.