Sabbin zarge-zarge kan jaridar News of the world ta Burtaniya

Wani wurin da ake sayar da jaridu
Bayanan hoto,

Wani wurin da ake sayar da jaridu

Sabbin zarge zarge akan dubarun da basu dace ba akan wani kamfanin yada labarai na News International sun kunno kai, yayinda Majalisar dokokin Birtaniya ke shirin tafka mahawara akan batun.

Hakan ya biyo bayan cewa, daya daga cikin jaridun kamfanin wato News of the World, ta bada kudi domin saurarar bayanan wayar salular wata yarinya da aka yiwa kisan gilla wato Milly Dowler a lokacin data bace, abun da kuma ya sa iyalinta tunanin cewa tana nan a raye.

Sai dai bayanan baya-bayanan na nuni da cewa akwai allaka ta siyasa wacce ta sabawa dokokin aikin jarida.

kamfanin News interntaional ya fitar da wasu sakonin e mail ga 'yansanda dake nuni da cewa tsohon editan jaridar News of the World Andy Coulson ya umurci a biya 'yansanda kudi domin samun bayanai daga wurinsu abun da ya sabawa doka.

Mr Coulson daga baya ya sami mukamin siyasa a matsayin Directan sadarwa na firaministan Birtaniya David Cameron .

Sai dai duk da cewa Mr Coulson ya ajiye mukaminsa a watan janairun da ya gabata amma hakan zai janyo tambayoyi akan hukuncin da Mr Cameron ya yi amfani da shi wurin daukar sa aiki