An kama wasu da ake zargin 'yan Boko Haram ne

Tsohon shugaban Boko Haram Muhammad yusuf
Image caption A shekara ta 2009 ne jami'an tsaro suka kashe Muhammad Yusuf, shugaban kungiyar

Hukumar tsaro ta farin kaya a Najeriya (SSS), ta ce ta kama wasu mutane fiye da 100 wadanda ta ke zargin 'ya'yan kungiyar Boko Haram ne.

Hukumar ta kuma ce ta bankado wani yunkuri na nada bama-bamai kimanin watanni daya da rabi da suka gabata. Hare-haren sari-ka-noke kan jami'an 'yan sanda ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 150 tun farkon bana - mafi yawanci a Arewa maso Gabashin kasar.

Kungiyar Boko Haram ta dauki alhakin mafi yawan hare-haren.

Rashin tsaron da ake fama da shi a wasu sassan arewacin kasar dai ya maye gurbin tashe-tashen hankulan da aka saba gani a yankin Niger Delta mai arzikin mai - inda a yanzu yankin ya zamo mafi barazana ta fuskar tsaro ga Najeriya a 'yan kwanakin nan.

'Amfani da dabaru'

"Wani sumame da jami'an SSS suka kai a jihohin Bauchi da Borno da Kano da Kaduna da Yobe da Adamawa, ya yi sanadiyyar cafke wasu 'ya'yan kungiyar Boko Haram," a cewar wata sanarwa da Hukumar SSS ta fitar.

Kungiyar ta Boko Haram ta dauki alhakin harin bom din da aka kai da mota a hedkwatar 'yan sandan kasar da ke Abuja. Kuma akwai tsoron kungiyar ka iya fadada hare-haren na ta zuwa karin wasu sassan kasar idan ba a dakile ta ba.

Hukumar SSS ta ce wasu daga cikin wadanda ake zargin na taimakawa Hukumar wajen bincike kuma ba za a hukuntasu ba.

"Shugaba Goodluck Jonathan ya yi alkawarin yin amfani da dabaru wajen tunkarar 'ya'yan kungiyar," a cewar sanarwar.

Masu adawa na zargin jami'an tsaron kasar da kasa tunkarar hare-haren na kungiyar Boko Haram da za a iya cewa sun zamo ruwan dare musamman ma a garin Maiduguri.

Ita dai Boko Haram tana fafutukar kafa tsarin shari'ar musulunci ne a yankin Arewacin kasar, duk da cewa jama'ar yankin da dama ba su yi na'am da hanyoyin da kungiyar ke bi ba wajen cimma bukatun na ta.

Ana danganta matsalolin tashin hankalin da ake samu a yankin da talauci, wanda ya yiwa mafi yawan jama'ar yankin katutu.

Hukumar SSS ta ce ta gano tare da lalata wasu bama-bamai 12 tun daga karshen watan Mayu, mafi yawancinsu a garin Kaduna, sannan ta nemi jama'a da su kara sa ido.

Duka shugaba Jonathan da kuma gwamna Kashim Shatima na jihar Borno, sun nemi kungiyar da ta amshi tayin afuwa domin a fara tattaunawa kan yadda za a kawo karshen rikicin.