Yan ci rani kusan 200 sun hallaka a Sudan

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Taswirar 'jan teku

Kamfanin dillancin labaru na kasar Sudan ya ce mutane dari daya da casai'n da bakwai ne suka hallaka a cikin 'jan teku bayan da jigrin ruwan da suke ciki ya kama da wuta .

Ya ce wasu jami'an kasar da ba'a bayana sunansu ba sun ce jirgin ruwan ya cika makil da bakin haure dake kokarin shiga ciki kasar Saudiya, kuma an ceto mutane uku.

Bugu da kari kamfanin ya ce dukkanin mutanen dake cikin jirgin ruwan 'yan kasashen waje ne .

Ya kuma ce ana cigaba da kokarin ceto sauran mutanen da suka rayu dake cikin jirgin ruwan.

Hukumomin Sudan sun ce sun yi nasarar capke wani jirgin ruwa me dauke da fasinjoji 247 .

Sun ce galibinsu daga kasashen Chadi, Nigeria da Somalia da kuma Eriterea ne suka fito.