Gwamnatin Syria ta keta hakkin bil'adama

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Masu zanga-zanga a kasar Syria

Kungiyar kare hakkin dan adam ta Amnesty International ta ce dakarun gwamnatin kasar Syria sun aikata laifukan da suka shafi take hakkin dan -adam, a irin matakan da suke dauka kan masu zanga zangar nuna kin jinin gwamnati a garin Tell -Kalak dake kan iyaka a cikin watan Mayun shekarar da ake ciki.

Rahotan na amnesty ya zargi dakarun kasar da aikata miyagun laifuka da suka hada da kisa da azabtarwa da kuma tsare mutane daya wuce ka'ida.

Wakilin BBC yace kungiyar Amnesty ta tattara bayananta ne daga 'yan kasar Syrian da suka tsere zuwa Lebanon, kuma kowane iyali da tayi hira dashi, ya bada labarin cewar yana da akalla dan- uwa guda da ake tsare dashi.

Gwamnatin Syrian dai bata ce komai ba dangane da wannan rahotan.