Al-Shabab ta amince a kai agaji Somalia

Al-Shabab ta amince a kai agaji Somalia Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Jama'a da dama ne suka kauracewa fari a kasar

Kungiyar Musulunci ta Somalia al-Shabab ta janye haramcin da ta sanya na hana kungiyoyin agaji na kasashen waje shiga kasar, yayin da ake fama da mummunan fari.

Al-Shabab ta sanya haramcin ne a shekara ta 2009, tana zarginsu da cewa makiya musulunci ne.

Amma yanzu ta ce dukkan kungiyoyin na "Musulmi ko wadanda ba na musulmi ba" za su iya bada agaji idan "ba su da wata boyayyiyar manufa".

Kusan kashi 25 cikin dari ne na 'yan Somalia suka bar gidajensu saboda fari, inda suke kaura zuwa makwafciyar kasar Kenya.

Mai magana da yawun al-Shabab, Sheik Ali Mohamud Rage, ya ce kungiyar ta kafa kwamiti da zai duba matsalar farin, kuma kowacce kungiyar agaji wajibi ne ta yi aiki da kwamitin.

Jin kunya

"Ko musulmai ne ko ba musulmai ba ne, in dai suna bukatar taimakawa ne to su tuntubi kwamitin zai hada su da mutanen," kamar yadda Mr Rage ya fada a wani taron manema labarai a birnin Mogadishu.

"Duk wanda ke da wata manufa a kasa domin cutar da jama'armu to za mu hana shi shiga," a cewarsa.

Masu sharhi sun ce al-Shabab ta dauki matakin ne sakamakon abin kunyar da ya faru inda jama'a ke tururuwar barin kasar domin neman abinci.

Al-Shabab ce ke iko da yawancin Kudanci da Tsakiyar Somalia.