Sabbin zarge-zarge kan jaridar News of the world

Hakkin mallakar hoto PA
Image caption Andy Coulson tsohon editan News of the World

Lauyoyin 'yan uwan sojojin kasar Birtaniya da aka kashe a kasashen Iraki da kuma Afghanistan sunce 'yan sanda sun yiwa wadanda suke karewa gargadi da cewar me yuwa jaridar News of the world na satar bayanan wayoyinsu.

Sai dai kamfanin News Co-oporation mai mallakar jaridar yace zai yi matukar mamaki idan har wadanan zarge zarge suka zamanto gaskiya, a saboda haka ne mai mallakar kamfanin Rupert Murdoch yace ya bada umarnin a baiwa 'yan sanda cikakken goyan bayan da suke bukata domin gudanar da bincike

A wata mahawara da ba'a saba ganin irinta ba a Majalisar dokokin kasar Birtaniya dangane da wannan batu firaministan kasar David Cameron ya fadawa majalisar cewar yana goyan bayan kiraye kirayen da ake na gudanar da bincike ga abinda ya kira, zarge- zarge na abin kunya.

Wani mai magana da yawun 'yan adawa a Birtaniya dai yace wannan lamari dake faruwa, rashin da'a ne.