An haramta amfani da babura a Maiduguri

Wadanda ake zargi Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Wadanda ake zargi

Gwamnatin jihar Borno a Nijeriya, ta kafa dokar hana amfani da babura dungurungun a cikin birnin Maiduguri da Karamar Hukumar Jere. Hukumomi sun ce dokar ta zama wajibi, bisa la'akari da irin kalubalen da ake fuskanta kan harkokin tsaro.

Galibi 'yan kungiyar Jama'atu Ahlil Sunna lidda'awati wal jihad, da aka fi sani da suna Boko Haram, suna amafani ne da babura wajen kai hare hare musamman a birnin Maiduguri. Gwamatin jihar Bornon ta bayyana cewar zata samar da wasu ababan hawan da zasu maye gurbin baburan da ta ce sun zama tamkar annoba a jihar.

A waje daya kuma 'ya 'yan kungiyar sun shaidawa BBC cewar sune ke da alhakin kai hare-haren da aka kai jiya a Maiduguri da kuma na Bauchi.

Haka nan kuma sun nemi tsaffin gwamnonin jihohin Borno da Gombe da kuma gwamnan Bauchi mai ci a yanzu, wadanda suka nemi gafara daga kungiyar da su cika sauran sharudda biyun da kungiyar ta gicciya musu.

Sauran sharuddan kuwa kamar yadda kakakin kungiyar Abu Zaid ya bayyana sune su yi watsi da abun da suka kira tsari na kafirci, su kuma taimakawa addinin Islama.