Wes Brown ya koma Sunderland

Image caption Wes Brown

Sunderland ta kammala siyan dan wasan bayan Manchester United Wes Brown.

Brown, mai shaikarun haihuwa 31, ya cimma yarjejeniyar takawa kungiyar Sunderland leda na tsawon shekaru hudu.

Har yanzu dai kungiyar ta Sunderland na neman abokan wasansa biyu wato John O'Shea da Darron Gibson.

Brown dai ya fara takawa United leda ne a shekarar 1998 kuma ya takawa kungiyar leda sau 361.

Kocin Sunderland Steve Bruce ya ce: "Muna matukar farincikin da zuwan Brown kungiyar mu, kuma muyi imanin cewa kwarewarsa za ta taimakawa kungiyar."