Mai yiwuwa a tsare Andy Coulson a yau

Image caption Andy Coulson

Kamfanin News International ya yi shelar rufe jaridar The News of the World, sakamakon cece- kucen da badakalar satar bayanan wayar salula ta janyo.

A ranar Lahadi mai zuwa ne dai za a buga jaridar ta karshe.

Shugaban kamfanin News International James Murdoch ya amince da cewa jaridar ta gaza gano musababbin abin da ya kira kuran- kuran da ta rika maimaitawa .

Jaridar The Guardian wacce ita ce fasa-kwai dangane da satar bayanan wayoyin salula ta ce tsohon editan jaridar News of the World Andy Coulson, wanda daga baya ya yi aiki a matsayin mai baiwa Firaministan Birtaniya David Cameron shawara kan harkokin sadarwa za a kama shi idan an jima a yau bisa tuhumar da ake masa akan cewa yanada masaniya dangane da batun satar bayanan wayoyin salula.

Ko da yake Mr Coulson ya sha musanta wannan zargi.

A yau ne dai gwamnatin kasar za ta kammala tattaunawar neman shawara akan matakin da za a dauka , sai dai idan an yi la'akari da dubban sakonnin mutane da za a karanta akwai yiwuwar cewa matakin zai dauki lokaci.