Ta yaya 'yancin Sudan ta kudu zai shafi Sudan?

Ta yaya 'yancin Kudancin Sudan zai shafi Sudan? Hakkin mallakar hoto other
Image caption Man fetur na daga cikin abubuwa masu muhimmanci a makomar kasashen biyu

Sudan dai za ta kirkiro sabbin kasashe biyu ne ba daya ba. Sabuwar kasar Sudan ta kudu za ta fuskanci kalubale iri iri, yayin da Sudan itama za ta shiga wani yanayi.

Dole Khartoum ta san yanda za ta yi ba tare da rijiyoyin man da ke kudanci, tare kuma da kokarin magance rikicin da ake yi a yankin Darfur da kuma rikicin kudancin Kordofan da ma wasu wuraren.

Fiye da haka kuma an yi ta muhawara game da Sudan, wani lamari da kasashen duniya suka damu kuma suke zuba ido akai.

'Yancin kan Kudanci zai shafi rage jiji-da-kan da wasu ke da shi kafin wannan lokacin, musamman Shugaba Omard Al Bashir game da cewa kasar ita ce mafi girma a nahiyar Afirka.

Jami'an sa kamar mai magana da yawun jam'iyyar da ta National Congress Party, Ibrahim Ghandour ya nanata cewa matsayin shugaban kasar ya karu tun da shi ne ya kawo karshen yakin basasar da aka yi a tsakanin arewa da kudu.

Rasa arzikin mai

Mista Ghandour dai ya amince da cewa Kudancin Sudan ce babbar matsalar Khartoum, kuma zaman dar dar din da ke tsakaninsu abu ne da ba zai gushe ba.

Sai dai ya amince da cewa Sudan za ta shiga mawuyacin yanayi, duk da dai ya musanta cewa alhakin hakan ya rataya akan jam'iyyarsa.

Ya kara da cewa: "akwai matsaloli a Sudan, wanda masu jari na kasashen waje sun taimaka, sannan kuma ga 'yan kasa da ke shiga cikin rikicin a saboda neman iko."

Hakkin mallakar hoto other
Image caption Kayan masarufi sun tashi a Sudan

Bugu da kari yanayin tattalin arzikin kasar abin damuwa ne akai.

A cikin kimanin shekaru goma da suka shude, Khartoum ta samu habakar mai, sai dai kimanin kashi uku bisa hudu na man daga bangaren Kudu yake.

Karkashin yarjejeniyar zaman lafiyar da aka cimma, Khartoum da Juba za su raba arzikin man kudancin ne daidai.

'Kayan masarufi'

"watanni biyu da suka wuce komai na da arha, amma yanzu abubuwa sun tashi, ana sayar da nama fan 12, amma yanzu fan 20 ne, yayin da sukari ya ninka," a cewar Muhamed, yana sayayya a garin Omdurman.

"Muna korafi ne a kan hauhawar farashi."

Hakan ya haifar da tunanin samun bore a kasar makamancin wanda ya kifar da gwamnatoci biyu a baya.

"Wannan ya yi kama da abin da ya faru a 1964 da 1985," a cewar Haj Hamad, wani masanin tattalin arziki.

Sai dai jami'an gwamnatin Sudan sun yi Allah wadai da wannan hasashen, suna masu cewa ainahin tushen tattalin arzikin kasar na da kwari.