Najeriya ta daure 'yan kasar China biyu

Image caption Taswirar Najeriya

A Najeriya, Wata babbar kotu a Lagos, ta yankewa 'yan kasar China da Taiwan biyu hukuncin dauri a gidan yari.

Mr. Fong Chui Sen dan Taiwan da Mr. Riachard Wang dan kasar China kowanne zai shafe tasown shekara 15 a gidan kasu.

A sa'adda mutane ukku 'yan Naijeriya nan, Alhaji Muhammed Inuwa, ,Ezeala Kinsley da kuma Godswill Asonugha da ake zargi da taimakawa 'yan China da Taiwan shigo da hodar Iblis ta wanke su, ba tare da samun su da wani laifi ba.

A bara ne dai hukumar NDLEA mai yaki da fataucin miyagun kwayoyi ta kama mutanen da shigo hodar Ibilis dag Chile, mai nauyin kilogram 450. kwatankwacin naira biliyon hudu kudin Naijeriya.

Safarar da hodar Ibilis dai ta zama ruwan dare a duniya, inda masu safararta ke ratsawa ta Naijeriya wajen fita da ita kasashen Turai da Amirka.